<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>A Mulkinka, Ubangiji LW323</title>
<lyrics>[V1]
 1) A mulkinka, Ubangiji,
 Za a tara dangogi,
 Harsuna dabam dabam kuwa,
 Suna yabon Almasihu.

[V2]
 2) Kewaye da Ubangiji,
 Cerabim da Sarafim
 Duk sun cika haikalinsa,
 Suna rera yabonsa.

[V3]
 3) Darajarka, Ubangiji,
 Ta ƙawata duniyan nan.
 Girma, yabo, mulki, iko,
 Naka duk, Ubangiji.

[V4]
 4) Mala'iku cikin Sama,
 Tare da Ekklesiyarka,
 Suna rera waƙar yabo
 Zuwa Ɗan Maɗaukaki.

[V5]
 5) Ɗaukaka ga Allah Uba,
 Mulki kuwa ga Allah Ɗa,
 Iko zuwa Allah Ruhu,
 Yabo zuwa Triniti.</lyrics>
<hymn_number>323</hymn_number>
</song>